15 Oktoba 2015 - 06:46
Amurka da Rasha na tattaunawa kan hare-hare su a Syria

Amurka na zaman tattaunawa da Rasha kan hare-haren da suke kai wa Syria gudun karo da juna a Sararrin Samaniya, zaman da ke zuwa bayan Rasha ta kaddamar da sabbin hare-hare 40 kan moboyar ISIS da ke Syria a kasa da Sa’o’i 24.

Sakataren Ma’aikatar tsaron Amurka Ashton Carter ya ce tattaunawarsu na yau zai mayar da hankali ne kan hanyoyin kawar da matsala a hare-haren da bangarorin 2 ke kaiwa kan mayakan ISIS a Syria

Carter ya ce duk da dai suna bayyana shakunsu kan Rasha, ganawar ya zama tilas domin gudun karo da juna.

Tattaunawar Amurka da Rasha na zuwa ne, bayan rahotanni a yanzu na bayyana tasirin da harin Rasha ke yi kan ISIS sama da wanda Amurka da kaweyanta ke kaiwa kasar sama da shekara 1.

Ko a yau sai dai gwamnatin Moscow ta sanar da kaddamar da sabbin hare-hare 40 a yankin Aleppo, Idlib, Latakia da Dier Ezzor kan mayakan.

Sai dai har yanzu Amurka na jadada cewa harin Rasha ba yana zuwa kan ‘yan ta’ada ba ne. 289